To, 'yan'uwa, muna yi muku umarni da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku fita daga sha'anin kowane ɗan'uwa malalaci, wanda ba ya bin ka'idodin da kuka samu a wurinmu.
Ga marasa Shari'a kuwa, sai na zama kamar marar Shari'a, ba cewa ba wata shari'ar Allah da take iko da ni ba, a'a, shari'ar Almasihu na iko da ni, domin in rinjayi marasa Shari'a ne.
Daga ƙarshe kuma 'yan'uwa, muna roƙonku, muna kuma yi muku gargaɗi saboda Ubangiji Yesu, cewa kamar yadda kuka koya a wurinmu, irin zaman da ya dace da ku, ku faranta wa Allah rai, kamar yadda yanzu ma kuke yi, to, sai ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske,