Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tessalonikawa 2:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Ya ku 'yan'uwa, kuna iya tunawa da wahala da famar da muka sha, har muna aiki dare da rana, don kada mu nauyaya wa kowane ɗayanku, duk sa'ad da muke yi muku bisharar Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Ba shakka kuna iya tunawa, ’yan’uwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku wa’azin bisharar Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tessalonikawa 2:9
35 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da nake a wurinku kuma nake zaman rashi, ban nauyaya wa kowa ba, domin 'yan'uwan da suka zo daga Makidoniya su ne suka biya mini bukata. Saboda haka, na ƙi nauyaya muku ta kowace hanya, ba kuwa zan nauyaya muku ba.


Da yake kuma sana'arsu ɗaya ce, maɗinkan tanti ne, ya sauka a wurinsu, suka yi ta aiki tare.


Ina gode wa Allah, wanda nake bauta wa da lamiri mai tsabta, kamar yadda kakannina suka yi, duk sa'ad da nake tunawa da kai a cikin addu'ata ba fāsawa.


Gwauruwa marar mataimaki kuwa, mai zaman kaɗaici, ta dogara ga Allah ke nan, tana nacewa ga roƙon Allah, tana addu'a dare da rana.


Saboda wannan maƙasudi muke wahala, muke ta fama, domin mun dogara ne ga Allah Rayayye, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman masu ba da gaskiya.


Ba mu kuwa taɓa neman girma ga mutane ba, ko a gare ku, ko ga waɗansu, ko da yake da muna so, da mun mori ikon nan namu na manzannin Almasihu.


Ina kuma hakkina? To, ga shi. A duk lokacin da nake yin bishara, sona in yi ta a kyauta, kada in ƙurashe halaliyata a game da bishara.


Amma ni kam, ban mori ko ɗaya daga cikin halaliyan nan ba, ba kuma ina rubuta wannan ne, don a yi mini haka ba. Ai, gara in mutu a kan wani ya banzanta mini fahariyata.


Saboda haka sai ku zauna a faɗake, ku tuna, shekara uku ke nan ba dare ba rana, ban fasa yi wa kowa gargaɗi ba, har da hawaye.


Ga abincin da ake shiryawa kowace rana, sa ɗaya, da tumaki shida kyawawa, da kuma kaji. A kowace rana ta goma akan kawo salkunan ruwan inabi masu yawa, amma duk da haka ban karɓi albashin da akan ba mai mulki ba, domin wahala ta yi wa mutane yawa.


Waɗanda suka riga ni mulki sun nawaita wa mutane. Sun yi ta karɓar abinci da ruwan inabi daga gare su, banda shekel arba'in kowace rana domin abinci da ruwan inabi. Har ma barorin masu mulki sun nawaya wa mutane. Amma ni ban yi haka ba, saboda ina tsoron Allah.


bisa ga bishara mai daraja ta Allah abar yabo, wadda aka danƙa mini.


Dare da rana muna nacin addu'a ƙwarai mu sami ganinku ido da ido, mu kuma cikasa abin da ya gaza wajen bangaskiyarku.


Amma ko da yake dā ma can mun sha wuya, an kuma wulakanta mu a Filibi, kamar yadda kuka sani, duk da haka da taimakon Allahnmu muka sanar da ku bisharar Allah gabagaɗi, amma sai da matsanancin fama.


ba ma fāsa tunawa da aikinku na bangaskiya a gaban Allahnmu, Ubanmu, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begen ku mara gushewa ga Ubangijinmu Yesu Almasihu.


Ko sa'ad da nake Tasalonika ma, kun aiko mini da taimako ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba.


da shan dūka, da shan ɗauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rasa barci, da kuma rasa abinci.


Guminmu muke ci. In an zage mu, mukan sa albarka. In an tsananta mana, mukan daure.


ta wurin ikon mu'ujizai, da abubuwan al'ajabai, da kuma ta wurin ikon Ruhun, har dai daga Urushalima da kewayenta, har zuwa Ilirikun, na yi bisharar Almasihu a ko'ina.


da ya sa ni bawan Almasihu Yesu ga al'ummai, ina hidimar bisharar Allah, domin al'ummai su zama hadaya mai karɓuwa a gare shi, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.


Daga Bulus, bawan Yesu Almasihu, manzo kirayayye, keɓaɓɓe domin yin bisharar Allah,


Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne?


da mijinta ya mutu kuma ta yi zaman gwauranci har shekara tamanin da huɗu. Ba ta rabuwa da Haikalin, tana bauta wa Allah dare da rana ta wurin yin addu'a da azumi.


Da ma kaina ruwa ne kundum, Idanuna kuma maɓuɓɓuga ne, Da sai in yi ta kuka dare da rana, Saboda an kashe jama'ata!


Ya Ubangiji Allah, Mai Cetona, Duk yini ina ta kuka, Da dare kuma na zo gare ka.


Ka hukunta ni dare da rana, ya Ubangiji, Ƙarfina duka ya ƙare sarai, Kamar yadda laima yake bushewa, Saboda zafin bazara.


Amma ni ban mai da raina a bakin kome ba, bai kuma dame ni ba, muddin zan iya cikasa tserena da kuma hidimar da na karɓa gun Ubangiji Yesu, in shaidar da bisharar alherin Allah.


Na sha fama, na sha wuya, na sha rashin barci, na sha yunwa da ƙishirwa, sau da yawa na rasa abinci, na sha sanyi da huntanci.


Ka ba mu izini mu tafi Kogin Urdun, domin mu saro gumagumai a can, mu ƙara wa kanmu wurin zama.” Sai ya ce, “Ku tafi.”


Ta sani akwai riba a cikin kasuwancinta. Fitilarta na ci dare farai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ