Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tessalonikawa 2:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Saboda wannan ne kuma muke gode wa Allah ba fasawa, domin sa'ad da kuka karɓi Maganar Allah ta bakinmu, ba ku karɓe ta kamar maganar mutum ce ba, sai dai ainihin yadda take, Maganar Allah, wadda take aiki a cikin zuciyarku, ku masu ba da gasikya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, sa’ad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tessalonikawa 2:13
41 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin Maganar Allah rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki, ta fi kowane irin takobi kaifi, har tana ratsa rai da ruhu, da kuma gaɓoɓi, har ya zuwa cikin ɓargo, tana kuma iya rarrabe tunanin zuciya da manufarta.


Ashe, bangaskiya ta wurin jawabin da ake ji take samuwa, jawabin da ake ji kuma ta Maganar Almasihu yake.


Gama sāke haifuwarku aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, wato, ta Maganar Allah rayayyiya dawwamammiya.


Maganar Ubangiji kuwa dawwamammiya ce,” Ita ce maganar bishara da aka yi muku.


Kamar jariri sabon haihuwa, ku yi marmarin shan madara marar gami mai ruhu, domin ku girma da shi, har ya kai ku ga samun ceto,


Amma ya ce, “I, amma albarka tā fi tabbata ga waɗanda suke jin Maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.”


Da al'ummai suka ji haka, suka yi farin ciki, suka ɗaukaka Maganar Ubangiji, ɗaukacin kuma waɗanda aka ƙaddara wa samun rai madawwami suka ba da gaskiya.


Duk mai ƙwallafa sa zuciya gare shi haka, yana tsarkake kansa ke nan, kamar yadda shi yake Mai Tsarki.


Ko da yake rashin lafiyata ta hana ku sukuni, duk da haka ba ku nuna mini raini ko ƙyama ba, sai dai kuka yi na'am da ni kamar wani mala'ikan Allah, ko ma Almasihu Yesu kansa.


Mu dukanmu kuma, fuskokinmu ba lulluɓi, muna nuna ɗaukakar Ubangiji, kamar madubi, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji kuwa wanda yake ruhu, yana zartar da haka.


To, waɗannan Yahudawa kam, sun fi na Tasalonika dattaku, domin sun karɓi Maganar hannu biyu biyu, suna ta nazarin Littattafai kowace rana, su ga ko abin haka yake.


wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika.


Amma ya amsa musu ya ce, “Masu jin Maganar Allah, suna kuma aikata ta, ai, su ne uwata, su ne kuma 'yan'uwana.”


Saboda su ne nake miƙa kaina, domin su ma a tsarkake su cikin gaskiya.


“Wanda ya yi na'am da ku, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.


Ka tsarkake su cikin gaskiya. Maganarka ita ce gaskiya.


Koyanzu ma ku tsarkakku ne saboda maganar da na faɗa muku.


“To, misalin shi ne, irin Maganar Allah ne.


Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku.


Ina so ku tuna da yin faɗin annabawa tsarkaka, da kuma umarnin Ubangiji Mai Ceto ta bakin manzannin da suka zo muku.


Bisa ga nufinsa ya kawo mu ta maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunan fari na halittarsa.


Da dai suka ji maganar tashin matattu, sai waɗansu suka yi ba'a, amma waɗansu suka ce, “Game da wannan magana kam, mā sāke jin abin da za ka faɗa.”


Ɗaya daga cikin masu sauraronmu wata mace ce, mai suna Lidiya, mai sayar da jar hajja, mutuniyar Tayatira, mai ibada ce kuma. Ubangiji ya buɗe zuciyarta, har ta mai da hankali ga abin da Bulus ya faɗa.


Nan da nan kuwa na aika maka, ka kuma kyauta da ka zo. To, yanzu ga mu duk mun hallara a gaban Allah, domin mu ji duk irin abin da Ubangiji ya umarce ka.”


Waɗanda suka ya na'am da maganarsa kuwa aka yi musu baftisma. A ran nan kuma suka ƙaru da mutum wajen dubu uku.


To, da manzannin da suke Urushalima suka ji Samariyawa sun yi na'am da Maganar Allah, suka aika musu da Bitrus da Yahaya.


Wata rana taro suna matsarsa domin su ji Maganar Allah, shi kuwa yana tsaye a bakin Tekun Janisarata,


“Ba za mu kasa kunne ga jawabin da kake yi mana da sunan Ubangiji ba!


Zarubabel ɗan Sheyaltiyel kuwa, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukan sauran mutane, suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu, suka kuma yi biyayya da maganar annabi Haggai, kamar yadda Ubangiji Allahnsu ya faɗa masa. Mutane kuwa suka yi tsoron Ubangiji.


Ai kuwa, an yi mana albishir kamar yadda aka yi musu, sai dai maganar da aka yi musu ba ta amfane su da kome ba, don kuwa ba ta gamu da bangaskiya ga majiyanta ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ