1 Tarihi 9:2 - Littafi Mai Tsarki2 Waɗanda suka fara zama a biranen mallakarsu, su ne Isra'ilawa da firistoci, da Lawiyawa, da kuma ma'aikatan Haikali. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 To, na farkon da aka sāke zaunar da su a mallakarsu a garuruwansu, su ne waɗansu Isra’ilawa, firistoci, Lawiyawa da kuma masu hidimar haikali. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga lissafin ma'aikatan Haikali da suka komo. Zuriyar Ziha, da zuriyar Hasufa, da zuriyar Tabbawot Zuriyar Keros, da zuriyar Siyaha, da zuriyar Fadon Zuriyar Lebana, da zuriyar Hagaba, da zuriyar Akkub Zuriyar Hagab, da zuriyar Shamlai, da zuriyar Hanan Zuriyar Giddel, da zuriyar Gahar, da zuriyar Rewaiya Zuriyar Rezin, da zuriyar Nekoda, da zuriyar Gazam Zuriyar Ussa, da zuriyar Faseya, da zuriyar Besai Zuriyar Asna, da Me'uniyawa, da Nefushiyawa Zuriyar Bakbuk, da zuriyar Hakufa da zuriyar Harhur Zuriyar Bazlut, da zuriyar Mehida, da zuriyar Harsha Zuriyar Barkos, da zuriyar Sisera, da zuriyar Tema Zuriyar Neziya, da zuriyar Hatifa.