Jonatan, ɗan Saul kuwa, yana da ɗa, sunansa Mefiboshet, amma gurgu ne. Yana da shekara biyar sa'ad da aka kawo labarin mutuwar Saul da Jonatan daga Yezreyel. Sai mai renonsa ta ɗauke shi, ta sheƙa a guje. A sa'ad da take gudu sai ya faɗo, sanadin gurguntakar ke nan.
Kai, da 'ya'yanka maza, da barorinka za ku riƙa yi wa iyalin Saul noma, ku kawo musu amfanin domin su sami abinci, amma Mefiboshet kansa, zai riƙa cin abinci a teburina kullum.” (Ziba kuwa yana da 'ya'ya maza goma sha biyar, da barori ashirin.)
Da aka zo da Mefiboshet, ɗan Jonatan, wato jikan Saul, sai ya rusuna har ƙasa, ya yi gaisuwa. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!” Ya amsa, “Ranka ya daɗe, ga baranka.”