6 'Ya'yan Biliyaminu su uku ne, wato Bela, da Beker, da Yediyayel.
6 ’Ya’ya uku maza na Benyamin su ne, Bela, Beker da Yediyayel.
'Ya'yan Biliyaminu, maza, su ne Bela, da Beker, da Ashbel, da Gera, da Na'aman, da Ahiram, da Rosh, da Muffim, da Huffim, da Adar.
Mayaƙan da aka lasafta bisa ga asalinsu na dukan iyalan Issaka, su dubu tamanin da dubu bakwai ne (87,000), jarumawa ne sosai.
'Ya'yan Bela, maza, su biyar ne, wato Ezbon, da Uzzi, da Uzziyel, da Yerimot, da Iri. Su ne shugabannin gidajen kakanninsu, jarumawa ne su. An lasafta su bisa ga asalinsu, su dubu ashirin da biyu ne da talatin da huɗu (22,034).