“Ka sa sun ci al'ummai da mulkoki da yaƙi, Ƙasashen da suke maƙwabtaka da tasu. Suka ci ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon, Da ƙasar Bashan, inda Og yake sarki.
“Ubangiji ya ce, ‘Ku tashi, ku kama hanya, ku haye kwarin Arnon. Duba, na ba da Sihon Ba'amore, Sarkin Heshbon, da ƙasarsa a hannunku, ku fara mallakar ƙasar, ku yaƙe shi.
Yeriya shi ne shugaban zuriyar Hebron bisa ga asalinsu. A shekara ta arba'in ta sarautar Dawuda, sai aka bincika, aka tarar akwai ƙarfafan mutane, jarumawa a cikinsu, a Yazar ta Gileyad.