Sa'an nan sarki ya ci gaba da yi wa Zadok magana, ya ce, “Ka gani, ka koma birni lafiya, kai da Abiyata tare da 'ya'yanku biyu, wato Ahimawaz ɗanka, da Jonatan, ɗan Abiyata.
Ahimawaz ɗan Zadok kuma ya ce wa Yowab, “Ko mene ne zai faru dai, ka bar ni in bi bayan Bahabashen a guje.” Yowab ya ce masa, “Don me za ka tafi, ɗana, tun da yake ba za ka sami lada saboda labarin da za ka kai ba?”
Sa'ad da fādawan Absalom suka zo gidan, suka tambayi matar, “Ina Ahimawaz da Jonatan suke?” Sai ta ce musu, “Ai, tuni sun haye kogi.” Sa'ad da suka neme su ba su same su ba, sai suka koma Urushalima.
Jonatan da Ahimawaz suna jira a En-rogel. Wata baranya takan tafi ta faɗa musu saƙo, su kuma sai su tafi su faɗa wa sarki Dawuda, don kada a gan su suna shiga birnin.
Sa'an nan Hushai ya ce wa Zadok da Abiyata, firistoci, “Ga irin shawarar da Ahitofel ya ba Absalom da dattawan Isra'ila, ga kuma irin wadda ni na bayar.
Sai Azariya, babban firist na gidan Zadok, ya amsa masa, ya ce, “Tun lokacin da suka fara kawo sadakarsu a Haikalin Ubangiji, mun ci mun ƙoshi, abin da ya ragu kuwa yana da yawa, gama Ubangiji ya sa wa jama'arsa albarka, saboda haka abin da ya ragu a rumbu yana da yawa.”