Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 6:76 - Littafi Mai Tsarki

76 Daga na kabilar Naftali kuma an ba da Kedesh ta Galili duk da makiyayarta, da Hammon duk da makiyayarta, da Kartan duk da makiyayarta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

76 daga kabilar Naftali kuwa suka sami Kedesh a Galili, Hammon da Kiriyatayim, tare da wuraren kiwonsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 6:76
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Daga cikin rabon kabilar Naftali aka ba su birane uku, su ne, Kedesh ta Galili da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Hammon da wuraren kiwo nata, da Kartan da wuraren kiwo nata.


Sai ta aika a kirawo Barak, ɗan Abinowam, daga birnin Kedesh a ƙasar Naftali. Ta ce masa, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ba ka wannan umarni, ya ce, ‘Ka tafi ka tara mutanenka a Dutsen Tabor, ka kuma ɗauki mutum dubu goma (10,000), daga kabilar Naftali da ta Zabaluna.


Saboda haka suka keɓe Kedesh ta Galili a ƙasar tuddai ta Naftali, da Shekem ta ƙasar tuddai ta Ifraimu, da Kiriyat-arba, wato Hebron, ta ƙasar tuddai ta Yahuza.


da Sarkin Kedesh, da Sarkin Yakneyam a Karmel,


da Helkat duk da makiyayarta, da Rehob duk da makiyayarta.


Daga na kabilar Zabaluna, an ba sauran Lawiyawa, wato 'ya'yan Merari, maza, Rimmon duk da makiyayarta, da Tabor duk da makiyayarta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ