Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 6:71 - Littafi Mai Tsarki

71 Daga na rabin kabilar Manassa na gabas, an ba 'ya'yan Gershon, maza, Golan ta Bashan tare da makiyayarta, da Ashtarot duk da makiyayarta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

71 Mutanen Gershom suka sami waɗannan. Daga gidan rabin kabilar Manasse, sun sami Golan a Bashan da kuma Ashtarot, tare da wuraren kiwonsu;

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 6:71
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Aka ba iyalan Gershonawa na cikin Lawiyawa birane biyu daga cikin rabo na rabin kabilar Manassa. Biranen su ne, Golan tare da wuraren kiwo nata, cikin Bashan, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Ashtarot da wuraren kiwo nata.


A hayin Urdun, gabas da Yariko, suka keɓe Bezer ta jeji a kan tudu a cikin yankin kabilar Ra'ubainu, da Ramot cikin Gileyad ta kabilar Gad, da Golan cikin Bashan ta kabilar Manassa.


da dukan abin da ya yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin Urdun, wato Sihon, Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, wanda yake a Ashtarot.


Biranen su ne, Bezer cikin jeji a kan tudu domin Ra'ubainawa, da Ramot cikin Gileyad domin Gadawa, da Golan cikin Bashan domin Manassawa.


A lokacin kuwa ya riga ya ci Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, wanda yake zaune a Ashtarot, da Edirai.


da rabin Gileyad, da Ashtarot, da Edirai, wato garuruwan sarki Og a Bashan. Mutanen Makir ne, ɗan Manassa, aka ba su wannan bisa ga iyalansu.


Daga cikin rabin kabilar Manassa kuma an ba su Ta'anak duk da makiyayarta, da Bileyam duk da makiyayarta. An ba da waɗannan ga sauran iyalai na 'ya'yan Kohat, maza.


Daga na kabilar Issaka kuma an ba su Kishiyon duk da makiyayarta, da Daberat duk da makiyayarta,


Gershonawa kuwa suka karɓi birane goma sha uku ta hanyar jefa kuri'a daga iyalan kabilar Issaka, da kabilar Ashiru, da kabilar Naftali, da rabin kabilar Manassa a Bashan.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ