Sa'ad da suke gudun Isra'ilawa suna a gangarar hawan Bet-horon, sai Ubangiji ya jefe su da manyan duwatsu daga sama, har zuwa Azeka, suka mutu. Waɗanda suka mutu ta ƙanƙarar duwatsu sun fi waɗanda Isra'ilawa suka kashe da takobi.
Ubangiji kuwa ya sa suka gigice a gaban Isra'ilawa. Isra'ilawa suka kashe su da yawa a Gibeyon, suka runtume su ta hanyar haurawa zuwa Bet-horon. Suka yi ta karkashe su har zuwa Azeka da Makkeda.