Kamar yadda Ubangiji ya umarci Joshuwa, ya ba Kalibu, ɗan Yefunne, rabonsa a tsakiyar jama'ar Yahuza. Rabon da aka ba shi, shi ne Kiriyat-arba, wato Hebron. Arba shi ne uban Anak.
Gershonawa kuwa suka karɓi birane goma sha uku ta hanyar jefa kuri'a daga iyalan kabilar Issaka, da kabilar Ashiru, da kabilar Naftali, da rabin kabilar Manassa a Bashan.