Aikinsu shi ne su taimaki 'ya'yan Haruna, maza, gudanar da aiki cikin Haikalin Ubangiji, wato lura da farfajiyoyi da ɗakuna, da tsabtace tsarkakan abubuwa, da yin taimako cikin kowace hidimar Haikalin Ubangiji.
Aka ba iyalan Gershonawa na cikin Lawiyawa birane biyu daga cikin rabo na rabin kabilar Manassa. Biranen su ne, Golan tare da wuraren kiwo nata, cikin Bashan, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Ashtarot da wuraren kiwo nata.