Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 6:39 - Littafi Mai Tsarki

39 Asaf kuma shi ne shugaban ƙungiyar mawaƙa ta biyu. Shi ɗan Berikiya ne, ɗan Shimeya,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

39 da kuma Asaf ’yan’uwan Heman, waɗanda suka yi hidima a hannun damansa. Asaf ɗan Berekiya, ɗan Shimeya,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 6:39
33 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mawaƙa, na zuriyar Asaf, ɗari da arba'in da takwas.


Mawaƙa na zuriyar Asaf, mutum ɗari da ashirin da takwas.


Ya Allah, kada ka yi shiru, Kada ka tsaya cik, Ya Allah, kada kuma ka yi tsit!


Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah Mai Cetonmu, Ku raira yabbai ga Allah na Yakubu!


Ya Allah, arna sun fāɗa wa ƙasar jama'arka! Sun ƙazantar da Haikalinka tsattsarka, Sun bar Urushalima kufai.


Na ta da murya, na yi kuka ga Allah, Na ta da murya, na yi kuka, ya kuwa ji ni.


Muna yabonka, ya Allah, muna yabonka! Muna shelar sunanka mai girma, Muna kuwa faɗa abubuwan banmamaki da ka aikata!


Hakika, Allah yana yi wa Isra'ila alheri, Da waɗanda suke da tsarkin zuciya!


A dā a zamanin Dawuda da Asaf akwai shugaban mawaƙa, akwai kuma waƙoƙin yabo da na godiya ga Allah.


Da kuma Mattaniya ɗan Mika, jīkan Zikri, zuriyar Asaf, shi ne shugaba na farko na mawaƙan addu'a ta godiya. Bakbukiya, shi ne mataimakin Mattaniya. Ga kuma Obadiya ɗan Shemaiya, jīkan zuriyar Galal, zuriyar Yedutun.


Dukan Lawiyawa mawaƙa, wato su Asaf, da Heman, da Yedutun tare da 'ya'yansu maza da 'yan'uwansu, aka sa su su tsaya a gabashin bagade, suna sāye da lilin mai kyau, suna ta kaɗa kuge, da molaye da garayu, ga kuma firistoci ɗari da ashirin masu busa ƙaho tare da su.


Allah yana matsayinsa a taron jama'arsa, Yakan zartar da nufinsa a taron alloli.


Ka kasa kunne gare mu, ya Makiyayin Isra'ila, Ka ji mu, kai da kake shugaban garkenka, Da kake zaune a kan kursiyinka, a bisa kerubobi.


Ku kasa kunne ga koyarwata, ya ku jama'ata, Ku kula da abin da nake faɗa.


Allah sananne ne a Yahuza, Mashahuri ne kuma a Isra'ila.


Don me ka yashe mu haka, ya Allah? Za ka yi ta fushi da jama'arka har abada ne?


Allah Maɗaukaki, Ubangiji, ya yi magana, Yana kiran dukan duniya, daga gabas zuwa yamma.


Sa'an nan waɗansu 'ya'yan firistoci, masu busar ƙaho, su ne Zakariya ɗan Jonatan, jīkan Shemaiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, da Mikaiya, da Zakkur, daga zuriyar Asaf.


Shugaban Lawiyawan da yake a Urushalima, shi ne Uzzi ɗan Bani, jīkan Hashabiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, ɗan Mika daga zuriyar Asaf. Su ne mawaƙa a Haikalin Allah.


Sa'ad da maginan suka aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji, firistoci suna nan tsaye saye da rigunansu, suna riƙe da ƙahoni, Lawiyawa kuma 'ya'yan Asaf, suna riƙe da kuge domin su yabi Ubangiji, bisa ga umarnin Dawuda, Sarkin Isra'ila.


Mawaƙa, 'ya'yan Asaf, maza, suna wurinsu bisa ga umarnin Dawuda, da Asaf, da Heman, da kuma Yedutun maigani na sarki, matsaran ƙofofi kuma suna a kowace ƙofa, ba lalle sai su bar wurin hidimarsu gama 'yan'uwansu Lawiyawa sun shirya musu nasu.


Sai sarki Hezekiya tare da sarakunansa, suka faɗa wa Lawiyawa su yi ta raira yabo ga Ubangiji da kalmomin Dawuda, da na Asaf maigani. Da murna suka raira yabo, suka sunkuya suka yi sujada.


A tsakiyar taron sai Ruhun Ubangiji ya sauka a kan Yahaziyel ɗan Zakariya, ɗan Benaiya, ɗan Yehiyel, ɗan Mattaniya, Balawe, na 'ya'yan Asaf, maza.


Ƙungiyoyin masu tsaron ƙofofi ke nan. Na wajen Kora shi ne Shallum ɗan Kore, daga cikin iyalin Ebiyasaf.


Daga cikin 'ya'yan Asaf, maza, Zakkur, da Yusufu, da Netaniya, da Asharela, Asaf mahaifinsu ne yake bi da su, shi ne kuma mawaƙin sarki.


A wannan lokaci ne Dawuda ya fara sa Asaf da 'yan'uwansa su riƙa raira waƙoƙin yabo ga Ubangiji.


ɗan Izhara, ɗan Kohat, ɗan Lawi, ɗan Isra'ila.


Dawuda fa da shugabannin Lawiyawa suka zaɓi waɗansu daga cikin 'ya'yan Asaf, maza, da na Heman, da na Yedutun domin su raira waƙa da garayu, da molaye, da kuge. Ga waɗanda suka yi wannan hidima.


Kuri'a ta faɗo a kan iyalan Kohatawa. Sai Lawiyawa na zuriyar Haruna firist suka karɓi birane goma sha uku daga kabilar Yahuza, da kabilar Saminu, da kabilar Biliyaminu.


Daga cikin kabilar Yahuza da kabilar Saminu aka ba zuriyar Haruna waɗannan birane da aka ambata.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ