Waɗannan su ne waɗanda suka yi ta raira waƙoƙin, su da 'ya'yansu maza. Daga iyalin Kohat, Heman shi ne shugaban ƙungiyar farko ta mawaƙa, shi ɗan Yowel ne, ɗan Sama'ila,
“Daga cikin 'ya'ya maza na Isra'ila sai ka kirawo ɗan'uwanka Haruna tare da 'ya'yansa, Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar, su zama firistoci masu yi mini aiki.
Amma mai hadayar zai wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sa'an nan firist ya ƙone duka a kan bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
Kada kowa ya kasance cikin alfarwar sujada lokacin da Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki domin ya yi kafara don kansa, da gidansa, da dukan taron jama'ar Isra'ila, sai lokacin da ya fita.
Akwai wani mutum daga kabilar Ifraimu sunansa Elkana, yana zaune a Rama, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Shi ɗan Yeroham ne, jika ga Eliyab, na iyalin Nahat, daga zuriyar Zuf.
'Ya'yan Amram, maza, su ne Haruna, da Musa. Aka keɓe Haruna domin ya tsarkake abubuwa mafi tsarki, domin shi da 'ya'yansa za su ƙone turare a gaban Ubangiji, su yi masa hidima, su riƙa sa albarka da sunansa har abada.
Waɗannan suna da aikin da aka ba su na hidimar Haikalin Ubangiji bisa ga ka'idar da kakansu Haruna ya kafa musu, kamar yadda Ubangiji Allah na Isra'ila ya umarce shi.