Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 6:3 - Littafi Mai Tsarki

3 'Ya'yan Amram kuwa, su ne Haruna, da Musa, da Maryamu. 'Ya'yan Haruna, maza, su ne Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Yaran Amram su ne, Haruna, Musa da Miriyam. ’Ya’yan Haruna maza su ne, Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 6:3
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

'Ya'yan Haruna, maza, Nadab da Abihu kuwa kowannensu ya ɗauki faranti ya sa wuta, ya zuba turare a kai, ya miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba.


Amram ya auri Yokabed 'yar'uwar mahaifinsa, ta kuwa haifa masa Haruna da Musa. Amram ya rayu shekara ɗari da talatin da bakwai.


Musa kuwa ya ce wa Haruna da 'ya'yansa maza, waɗanda suka ragu, wato, Ele'azara da Itamar, “Ku ɗauki ragowar hadaya ta gari wadda aka yi hadaya ta ƙonawa da ita ga Ubangiji, ku ci ba tare da yisti ba a gefen bagaden, gama tsattsarka ne.


Sai Maryamu, annabiya, 'yar'uwar Haruna, ta ɗauki kuru cikin hannunta. Mata duka suka fita, suka bi ta da kuwaru suna ta rawa.


Gama na fito da ku daga ƙasar Masar, Na fanshe ku daga gidan bauta. Na aika muku da Musa, da Haruna, da Maryamu.


'Ya'yan Amram, maza, su ne Haruna, da Musa. Aka keɓe Haruna domin ya tsarkake abubuwa mafi tsarki, domin shi da 'ya'yansa za su ƙone turare a gaban Ubangiji, su yi masa hidima, su riƙa sa albarka da sunansa har abada.


Da Musa ya nemi bunsurun hadaya don zunubi sai ya tarar an ƙone shi. Ya kuwa yi fushi da Ele'azara da Itamar, 'ya'yan Haruna, maza, waɗanda suka ragu, ya ce,


“Daga cikin 'ya'ya maza na Isra'ila sai ka kirawo ɗan'uwanka Haruna tare da 'ya'yansa, Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar, su zama firistoci masu yi mini aiki.


Ubangiji ya ce wa Musa, “Ku zo wurina, kai, da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawa saba'in na Isra'ila. Ku yi sujada daga nesa kaɗan.


Haruna ya auri Elisheba, 'yar Amminadab 'yar'uwar Nashon. Sai ta haifa masa Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar.


'Yar'uwar jaririn kuwa ta ce wa Gimbiya, “In tafi in kirawo miki wata daga cikin matan Ibraniyawa da za ta yi miki renon ɗan?”


Ga 'yar'uwarsa kuma a tsaye daga nesa don ta san abin da zai same shi.


'Ya'yan Kohat, maza, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel.


Zuriyar Ele'azara daga tsara zuwa tsara, su ne Finehas, da Abishuwa,


Daga iyalin Uzziyel ɗari da goma sha biyu, Amminadab ne shugabansu.


'Ya'yan Kohat, maza, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel, su huɗu ke nan.


Na wajen Izhara, shi ne Shelomit, na wajen Shelomit, shi ne Yahat.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ