29 Zuriyar Merari bi da bi, su ne Mali, da Libni, da Shimai, da Uzza,
29 Zuriyar Merari su ne, Mali, Libni, Shimeyi, Uzza,
'Ya'yan Merari, maza kuwa, su ne Mali da Mushi. Waɗannan su ne iyalan Lawiyawa bisa ga gidajen kakanninsu.
Iyalan Merari su ne iyalin Maliyawa, da na Mushiyawa. Waɗannan su ne iyalan Merari.
'Ya'yan Gershon, maza kuwa, su ne Libni, da Shimai bisa ga iyalansu.
'Ya'yan Sama'ila, maza, su ne Yowel ɗan farinsa, na biyun shi ne Abaija.
da Shimeya, da Haggiya, da Asaya.
Sulemanu kuwa yakan ba Hiram alkama mudu dubu ashirin (20,000), da tattaccen man zaitun ma'auni dubu ashirin (20,000) kowace shekara domin ya ciyar da mutanensa.
Saboda haka Lawiyawa suka zaɓi Heman ɗan Yowel, da Asaf ɗan Berikiya daga cikin 'yan'uwansu. Daga iyalin Merari kuma aka zaɓi Etan ɗan Kishi.