Sarki Nebukadnezzar ya kama Yehozadak, ya tafi da shi tare da sauran jama'a zuwa zaman talala, sa'ad da Ubangiji ya ba da su a hannun Nebukadnezzar don su yi zaman talala.
Shugaban matsara kuma ya ɗauki Seraiya babban firist, da Zafaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar Haikali, ya tafi da su.