Da yardar rai manyan ma'aikatansa, sarakunansa, suka ba da gudunmawa ga jama'ar, da firistoci, da Lawiyawa. Hilkiya, da Zakariya, da Yehiyel, manyan ma'aikatan Haikalin Allah, suka ba firistoci abin yin hadaya don Idin Ƙetarewa, tumaki da awaki dubu biyu da ɗari shida (2,600), da bijimai ɗari uku.
Ya aika da wasiƙar ta hannun Elasa ɗan Shafan, da Gemariya ɗan Hilkiya waɗanda Zadakiya Sarkin Yahuza ya aika zuwa Babila, wurin Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Ga abin da wasiƙar ta ce.