Gādon kabilar Saminu yana cikin yankin ƙasar rabon kabilar Yahuza domin rabon kabilar Yahuza ya yi mata yawa, don haka kabilar Saminu ta sami gādo daga cikin tsakiyar gādon kabilar Yahuza.
Ibrahim ya tashi da sassafe, ya kuma ɗauki gurasa da salkar ruwa, ya bai wa Hajaratu, ya ɗora kafaɗarta. Sai ya ba ta ɗanta, ya sallame ta. Ta tafi ta yi ta yawo cikin jejin Biyer-sheba.
Shimai yana da 'ya'ya maza goma sha shida, da 'ya'ya mata shida, amma 'yan'uwansa ba su da 'ya'ya da yawa kamarsa. Iyalin Saminu ba su kai yawan na Yahuza ba.