11 Kalibu ɗan'uwan Shuwa, shi ne mahaifin Mehir wanda ya haifi Eshton.
11 Kelub, ɗan’uwan Shuha, shi ne mahaifin Mehir, wanda shi ne mahaifin Eshton.
Yabez ya roƙi Allah na Isra'ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, ka faɗaɗa kan iyakata, hannunka kuma ya kasance tare da ni, ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa ya biya masa bukatarsa.
Eshton kuwa shi ne ya haifi Bet-rafa, da Faseya, da Tehinna wanda ya kafa birnin Ir-nahash, zuriyar waɗannan mutane kuwa su suka zauna a Reka.