Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 3:15 - Littafi Mai Tsarki

15 'Ya'yan Yosiya, maza, su ne Yohenan ɗan farinsa, na biyu shi ne Eliyakim, na uku shi ne Zadakiya, na huɗu shi ne Yehowahaz,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 ’Ya’yan Yosiya maza su ne, Yohanan ɗan fari, Yehohiyakim ɗa na biyu, Zedekiya ɗa na uku Shallum ɗa na huɗu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 3:15
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Fir'auna-neko ya sarautar da Eliyakim ɗan Yosiya a matsayin tsohonsa. Ya sāke masa suna ya sa masa suna Yehoyakim. Ya ɗauki Yehowahaz ya tafi da shi Masar, can ya mutu.


Yehowahaz yana da shekara ashirin da uku sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Hamutal 'yar Irmiya na Libna.


Eliyakim yana da 'ya'ya biyu maza, su ne Yekoniya, da Zadakiya.


da a zamanin Yehoyakim ɗan Yosiya Sarkin Yahuza kuma, har ƙarshen shekara ta goma sha ɗaya ta Zadakiya ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, har zuwa lokacin da aka kai mazaunan Urushalima zaman talala a wata na biyar.


Gama haka Ubangiji ya ce a kan Yahowahaz, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, wanda ya gāji sarautar ubansa, Yosiya, wanda ya tafi ya bar wurin nan. Ba zai ƙara komowa nan ba.


Zadakiya ɗan Yosiya, wanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila ya naɗa Sarkin Yahuza, ya yi mulki a maimakon Yekoniya ɗan Yehoyakim.


Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya naɗa Mattaniya ɗan'uwan tsohon Yekoniya sarki a maimakon Yekoniya sa'an nan ya ba shi suna Zadakiya.


Jama'ar ƙasa kuwa suka ɗauki Yehowahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki. Ya gaji tsohonsa a Urushalima.


Da bazara sai sarki Nebukadnezzar ya aika aka kawo shi Babila tare da kayayyaki masu daraja na Haikalin Ubangiji. Ya kuma naɗa Zadakiya ɗan'uwan Yekoniya ya zama Sarkin Yahuza da Urushalima.


Domin haka ga abin da Ubangiji ya ce a kan Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, “Ba za su yi makoki dominsa ba, ko su ce, ‘Wayyo ɗan'uwanmu!’ ko, ‘Wayyo 'yar'uwarmu!’ Ba za su yi makoki dominsa ba, su ce, ‘Wayyo ubangidanmu!’ ko ‘Wayyo mai martaba!’


“Ni Ubangiji na ce, zan mai da Zadakiya Sarkin Yahuza, da sarakunansa, da sauran mutanen Urushalima da suka ragu a ƙasar, da mutanen da suka tafi Masar, kamar ruɓaɓɓen ɓauren nan da suka lalace har ba su ciwuwa.


A farkon sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ