Fādawansa kuwa suka ɗauko gawarsa a karusa daga Magiddo, suka kawo Urushalima, suka binne a kabarinsa. Sai jama'ar ƙasa suka naɗa Yehowahaz ɗan Yosiya sarki a matsayin tsohonsa.
Domin haka ga abin da Ubangiji ya ce a kan Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, “Ba za su yi makoki dominsa ba, ko su ce, ‘Wayyo ɗan'uwanmu!’ ko, ‘Wayyo 'yar'uwarmu!’ Ba za su yi makoki dominsa ba, su ce, ‘Wayyo ubangidanmu!’ ko ‘Wayyo mai martaba!’
Gama haka Ubangiji ya ce a kan Yahowahaz, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, wanda ya gāji sarautar ubansa, Yosiya, wanda ya tafi ya bar wurin nan. Ba zai ƙara komowa nan ba.
Yehoyakim yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarauta a Urushalima. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa.
Sai Fir'auna-neko ya sarautar da Eliyakim ɗan Yosiya a matsayin tsohonsa. Ya sāke masa suna ya sa masa suna Yehoyakim. Ya ɗauki Yehowahaz ya tafi da shi Masar, can ya mutu.