Amaziya yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara ashirin da tara yana mulki a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yehowaddin ta Urushalima.
Hosheya ɗan Ila kuwa ya ƙulla wa Feka ɗan Remaliya maƙarƙashiya, ya buge shi ya kashe shi, sa'an nan ya ci sarauta a shekara ta ashirin ta sarautar Yotam ɗan Azariya.
Yotam yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yerusha 'yar Zadok.
Sai Ubangiji ya buge shi da kuturta, ya kuwa zama kuturu har ran da ya rasu. Ya zauna a wani gida a ware. Sai Yotam ɗansa ya zama wakilin gidan, yana kuma mulkin jama'ar ƙasar.