Suka zo suka faɗa wa Yahuza da yaƙi. Suka washe dukan dukiyar da aka samu a gidan sarki, suka tafi da ita. Suka kuma kwashe 'ya'yansa, da matansa, ba wanda aka bar masa, sai Ahaziya autansa.
Don haka sai ya koma Yezreyel don ya yi jiyyar raunukan da aka yi masa a Rama, sa'ad da suka yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Ahaziya ɗan Yoram, Sarkin Yahuza, ya gangara don ya gai da Yehoram ɗan Ahab a Yezreyel wanda yake rashin lafiya.
Amma Yehosheba 'yar sarki Yoram, 'yar'uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin 'ya'yan sarki waɗanda aka kashe, ta ɓoye shi da mai renonsa, an yi ta renonsa cikin ɗaki. Da haka ta tserar da shi daga Ataliya, har ba a kashe shi ba.
Ahaziya, ɗan Ahab, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta sarautar Yehoshafat, Sarkin Yahuza. Ya yi sarautar Isra'ila shekara biyu.