10 Waɗannan su ne zuriyar Sulemanu, daga Rehobowam, sai Abaija, da Asa, da Yehoshafat,
10 Zuriyar Solomon su ne Rehobowam, da Abiya, da Asa, da Yehoshafat,
Sulemanu ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda, wato Urushalima, ɗansa Rehobowam ya gaji sarautarsa.
Yehoshafat ɗansa kuwa ya gāji gadon sarautarsa, ya kahu sosai gāba da Isra'ila.
Asa kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima, Ɗansa Yehoshafat ya gāji sarautarsa.
Abaija ya rasu, suka binne shi a Urushalima. Ɗansa Asa ya gāji sarautarsa.
Rehobowam kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Na'ama, ita kuwa Ba'ammoniya ce. Ɗansa, Abaija ya gāji sarautar.
Sarki Abaija kuwa ya rasu, suka binne shi tare da kakanninsa a birnin Dawuda. Ɗansa Asa shi ya gāji gadon sarautarsa. Ƙasar ta sami sakewa har shekara goma a zamaninsa.
A shekara ta goma sha takwas ta mulkin sarki Yerobowam, sai Abaija ya ci sarautar Yahuza.
Akwai yaƙi tsakanin Abaija da Yerobowam dukan kwanakin ransa.
Waɗannan duka su ne 'ya'yan Dawuda, maza, banda 'ya'yan ƙwaraƙwarai. Tamar ita ce 'yar'uwarsu.
da Yoram, da Ahaziya, da Yowash,