1 Tarihi 29:3 - Littafi Mai Tsarki3 Saboda kuma ƙaunar Haikalin Allahna da nake yi, shi ya sa na ba da zinariyata da azurfata domin Haikalin Allahna, banda wanda na riga na tanada saboda Haikali mai tsarki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Ban da haka ma, cikin sa zuciyata ga haikalin Allahna, yanzu na ba da ma’ajina na zinariya da azurfa saboda haikalin Allahna, fiye da kome na tanada saboda wannan haikali, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A halin yanzu dai na riga na yi iyakacin ƙoƙarina, har na tanada waɗannan abubuwa saboda Haikalin Allahna, wato zinariya saboda kayayyakin zinariya, azurfa saboda kayayyakin azurfa, tagulla saboda kayayyakin tagulla, baƙin ƙarfe saboda kayayyakin baƙin ƙarfe, itace kuwa saboda kayayyakin itace, da duwatsu da yawa masu daraja, da masu launi iri iri.