Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 28:9 - Littafi Mai Tsarki

9 “Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 “Kai kuma ɗana Solomon, ka san Allah na mahaifinka, ka kuma yi masa hidima da dukan zuciya da kuma yardar rai, gama Ubangiji yana binciken zuciya, yana kuma gane dukan aniyar tunani. In ka neme shi, za ka same shi; amma in ka yashe shi, zai ƙi ka har abada.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 28:9
79 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za ku neme ni ku same ni, idan kun neme ni da zuciya ɗaya.


Zan ba su zuciyar da za su sani ni ne Ubangiji. Za su kuwa zama jama'ata, ni kuwa zan zama Allahnsu, gama za su komo wurina da zuciya ɗaya.


Ku kuma jama'arsa, sai ku amince da Ubangiji Allahnmu da zuciya ɗaya, ku kiyaye dokokinsa da umarnansa, kamar yadda kuke yi a yau.”


sai ya fita ya taryi Asa, ya ce masa, “Ka ji ni, ya Asa, kai da dukan Yahuza da Biliyaminu, Ubangiji yana tare da ku idan kuna tare da shi. Idan kuwa kun neme shi, za ku same shi, amma idan kun rabu da shi, shi ma zai rabu da ku.


Waɗanda suka san ka za su amince da kai, ya Ubangiji, Ba za ka ƙyale duk wanda ya zo gare ka ba.


Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka kula da kyan tsarinsa, ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”


Allah Ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa lalle su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”


Ni Ubangiji nakan bincike tunani, In gwada zuciya, Domin in sāka wa kowane mutum gwargwadon al'amuransa, Da kuma gwargwadon ayyukansa.


Ka sa dukan abin da nake yi, Tun daga can nesa ka gane dukan tunanina.


Amma bari wanda zai yi fariya, ya yi fariya a kan cewa ya fahimce ni, ya kuma san ni. Ni ne Ubangiji mai yin alheri, da gaskiya, da adalci a duniya, gama ina murna da waɗannan abubuwa, ni Ubangiji na faɗa.”


Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko.


Ya ku mutanen Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji, Gama Ubangiji yana da shari'a da ku, ku mazaunan ƙasar. “Gama ba gaskiya, ko ƙauna, Ko sanin Ubangiji a ƙasar.


Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji’ ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”


Ba a ɓoye na yi magana ba, Ban kuwa ɓoye nufina ba. Ban ce jama'ar Isra'ila Su neme ni a kowace hanyar ruɗami ba. Ni ne Ubangiji, gaskiya kuwa nake faɗa, Ina sanar da abin da yake daidai.”


“Ka tuna da ni yanzu, ya Ubangiji, ina roƙonka, da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci, da zuciya ɗaya, na aikata abin da yake mai kyau a gabanka.” Sai ya yi ta rusa kuka.


Ya biya wa matalauta da masu bukata hakkinsu, Ya kuwa yi kyau. Abin da ake nufi da sanina ke nan, In ji Ubangiji.


Ubangiji ne ƙarfina da mafakata, Shi ne wanda ya cece ni. Wannan ne Allahna, zan yabe shi, Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.


Sai jama'a suka yi murna da ganin yadda suka bayar hannu sake, gama sun kawo sadakokinsu a gaban Ubangiji da zuciya ɗaya, shi sarki Dawuda kuma ya yi murna ƙwarai.


sai ka ji addu'arsa. Ka kasa kunne gare shi, a wurin zamanka a Sama, ka gafarta masa. Kai kaɗai ka san tunanin dukan mutane. Ka yi da kowa bisa ga abin da ya yi,


Dā kam, Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu yana umartar dukkan mutane a ko'ina su tuba,


Ba wata halittar da za ta iya ɓuyar masa, amma kowane abu a fili yake, a shanye sosai a gaban idon wannan da za mu ba da lissafi a gabansa.


Abin da nake yi ba zai zama laifi ba, Yaushe za ka zo wurina? Da zuciya mai tsabta zan zauna a gidana.


Ka tsai da muguntar mugaye, Ina roƙonka, ka sāka wa mutanen kirki. Kai Allah mai adalci ne, Kana kuwa auna tunanin mutane, da marmarinsu.


Sa'ad da yawan masifun nan da wahalan nan suka same su, to, waƙar nan za ta ba da shaida a kansu, gama zuriyarsu ba za ta manta da wannan waƙa ba, gama na san ƙudurin da suke yi kafin in kawo su ƙasar da na rantse zan bayar.”


Saboda haka, sai mu yi godiya domin mun sami mulkin da ba ya girgizuwa, ta haka kuma mu yi wa Allah sujada abar karɓa, tare da tsoro da tsananin girmamawa,


Ya yi abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji. Ya bi dukan halin kakansa, Dawuda, bai kauce dama ko hagu ba.


Sai suka yi addu'a, suka ce, “Ya Ubangiji, masanin zuciyar kowa, a cikin waɗannan mutum biyu ka nuna wanda ka zaɓa,


Yesu ya faɗa masa, faɗa ta uku, “Bitrus ɗan Yahaya, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki don a faɗar nan ta uku ya ce masa, “Kana sona?” Shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ai, ka san kome duka, ka kuwa sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina.


domin ya san zuciyar kowa, ba kuma sai wani ya shaidi mutum a wurinsa ba, domin shi kansa ya san abin da yake zuciyar ɗan adam.


Mutanena sun lalace saboda jahilci. Tun da yake sun ƙi ilimi, Ni ma na ƙi ku da zaman firist ɗina. Tun da yake kun manta da umarnan Allahnka, Ni ma zan manta da 'ya'yanku.


An nuna muku wannan don ku sani Ubangiji shi ne Allah, banda shi, ba wani kuma.


Domin shi Allah wanda ya ce, “Haske yă ɓullo daga duhu ya haskaka,” shi ne ya haskaka zukatanmu domin a haskaka mutane su san ɗaukakarsa a fuskar Yesu Almasihu.


Sa'ad da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce, “Ba zan ƙara la'anta ƙasa sabili da mutum ba, ko da yake zace-zacen zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa. Ba zan kuma ƙara hallaka kowane mai rai ba kamar yadda na yi a dā.


Ubangiji Allah ya ce, “A wannan rana tunani zai shiga cikin zuciyarka, za ka ƙirƙiro muguwar dabara,


Amma ya Ubangiji Mai Runduna, mai shari'ar adalci, Kakan gwada zuciya da tunani, Ka yarda mini in ga sakayyar da za ka yi mini a kansu, Gama a gare ka na danƙa maganata.


Zinariya da azurfa da wuta ake gwada su, zuciyar ɗan adam kuwa Ubangiji ne yake gwada ta.


Gama na ji kunya in roƙi sarki ya ba mu sojojin ƙasa da na doki su kāre mu daga maƙiya a hanya, da yake na riga na faɗa masa cewa, “Allah yana tare da dukan waɗanda suke nemansa, ikonsa da fushinsa mai zafi kuwa yana kan dukan waɗanda suke mantawa da shi.”


Tafi, ka tattara dattawan Isra'ila, ka faɗa musu, ‘Ubangiji Allah na kakanninku ya bayyana gare ni, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, ya ce, sosai ya ziyarce ku, ya kuma ga abin da ake yi muku a Masar.


Ya Ubangiji Mai Runduna, mai gwada adali, Mai ganin zuciya duk da tunani, Ka sa in ga sakayyar da za ka yi musu, Gama a gare ka nake kawo ƙarata.”


Ubangiji ne Mai Cetona, Shi ne garkuwata mai ƙarfi. Allahna, shi ne yake kiyaye ni, Lafiya nake sa'ad da nake tare da shi, Yana kiyaye ni kamar garkuwa, Yana kāre ni, ya ba ni lafiya.


Zan kashe 'ya'yanta tashi ɗaya, dukan ikilisiyoyi kuma za su sani Ni ne mai fayyace birnin zuciya. Zan kuma saka wa kowannenku gwargwadon aikinsa.


ku yi kiwon garken Allah da yake tare da ku, ba a kan tilas ba, sai dai a kan yarda, ba ma don neman ribar banza ba, sai dai da himma.


Don sa'ad da nake zagawa, na duba abubuwan da kuke yi wa ibada, har ma na tarar da wani bagadin hadaya da wannan rubutu a sama da shi cewa, ‘Saboda Allahn da ba a sani ba.’ To, shi wanda kuke yi wa sujada ba a tare da kun san shi ba, shi nake sanar muku.


Ku ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Da na ce ban san shi ba, da na zama maƙaryaci kamarku. Amma na san shi, ina kuma kiyaye magana tasa.


Yesu ya ga Nata'ala na nufo shi, sai ya yi zancensa ya ce, “Kun ga, ga Ba'isra'ile na gaske wanda ba shi da ha'inci!”


Zai ce mini, ‘Kai ubana ne da Allahna, Kai ne kake kiyaye ni, kai ne Mai Cetona.’


Sulemanu ya amsa ya ce, “Kai ne kake nuna ƙauna mai girma a koyaushe ga bawanka Dawuda, tsohona, domin ya yi tafiya a gabanka da aminci, da adalci, da tawali'u. Kai kuwa ka tabbatar masa da wannan ƙauna mai girma, ka kuma ba shi ɗa wanda zai hau gadon sarautarsa a wannan rana.


Amma zai ragargaza dukan wanda ya yi zunubi, ya tayar gāba da shi, zai kashe duk wanda ya rabu da shi.


Ga shi kuwa, Ubangiji na tsaye a kansa yana cewa, “Ni ne Ubangiji, Allah na Ibrahim, mahaifinka, da Ishaku, ƙasar da kake kwance a kai, zan ba ka ita da zuriyarka.


Domin mutum yana da niyyar bayarwa, bayarwarsa za ta zama abar karɓa ce, bisa ga yawan abin da yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.


Ku farka daga magagi, ku kama aikin adalci, ku daina yin zunubi. Waɗansu kam, ba su da sanin Allah. Na faɗi wannan ne don ku kunyata.


Ubangiji kuwa ya ga muguntar mutum ta ƙasaita a duniya, dukan zace-zacen tunanin zuciyarsa kuma mugunta ne kullayaumin.


Sai kowa yă bayar yadda ya yi niyya, ba tare da ɓacin rai ko tilastawa ba, domin Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.


sai ka kasa kunne ga addu'arsa. Ka ji daga Sama, wurin zamanka, ka amsa masa abin da ya roƙe ka, domin dukan mutanen duniya su san sunanka, su kuma yi tsoronka kamar jama'arka, Isra'ilawa, domin kuma su sani wannan Haikali da na gina wurin da za a yi maka sujada ne.


Ya rabu da Ubangiji Allah na kakanninsa, bai bi tafarkin Ubangiji ba.


Yanzu fa sai ku sa hankalinku da zuciyarku ga neman Ubangiji Allahnku. Ku tashi, ku gina wa Ubangiji Allah tsattsarkan wuri domin a kawo akwatin alkawari na Ubangiji, da tsarkakakkun tasoshin Allah a cikin Haikalin da aka gina saboda sunan Ubangiji.”


“Saboda haka a gaban dukan Isra'ila, wato taron jama'ar Ubangiji, da kuma gaban Allahnmu, sai ku kiyaye, ku bi dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki ƙasan nan mai kyau, ku kuma bar wa 'ya'yanku ita gādo har abada.


sa'an nan za ka ji daga wurin zamanka a Sama, ka yi gafara, ka kuwa sāka wa kowa bisa ga al'amuransa, wanda ka san zuciyarsa, gama kai kaɗai ne ka san zukatan mutane,


Amma kana fushi da zaɓaɓɓen sarkinka, Ka rabu da shi, ka yashe shi.


A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai.


“Ya Ubangiji, ka tuna, na bauta maka da aminci da biyayya, na kuma yi ƙoƙarin aikata abin da kake so in yi.” Sai ya fara kuka mai zafi.


“Yanzu fa, ya Isra'ilawa ga abin da Ubangiji Allahnku yake so a gare ku. Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku.


Sama'ila kuwa ya ce musu, “Kada ku razana, gama kun riga kun aikata wannan mugunta, duk da haka kada ku bar bin Ubangiji, amma ku bauta masa da zuciya ɗaya.


Sai annabi Shemaiya ya zo wurin Rehobowam da sarakunan Yahuza waɗanda suka tattaru a Urushalima saboda Shishak, ya ce musu, “Ubangiji ya ce kun yashe shi, don haka shi ma ya bashe ku a hannun Shishak.”


Allah ne mai kiyaye ni, Yakan ceci waɗanda suke yi masa biyayya.


Ka san zuciyata, Kakan zo gare ni da dare, Ka riga ka jarraba ni sarai, Ba ka kuwa sami mugun nufi a cikina ba. Na ƙudurta kuma bakina ba zai yi saɓo ba.


mahaifina yakan koya mini, yakan ce, “Ka tuna da abin da nake faɗa maka, kada ka manta. Ka yi abin da na faɗa maka za ka rayu.


Za ku same ni, ni Ubangiji na faɗa, zan mayar muku da arzikinku, in tattaro ku daga cikin dukan al'ummai da dukan wurare inda na kora ku, ni Ubangiji na faɗa, zan komo da ku a wurin da na sa a kwashe ku a kai ku zaman talala.’ ”


Sa'an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kaina, ya ce mini, “Ka ce, ‘In ji Ubangiji, haka kuke tunani, ku mutanen Isra'ila, gama na san abin da yake cikin zuciyarku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ