1 Tarihi 28:2 - Littafi Mai Tsarki2 Sarki Dawuda fa ya miƙe tsaye, ya ce, “Ku saurare ni, ku 'yan'uwana, da jama'ata. Na yi niyya a zuciyata in gina wa akwatin alkawari na Ubangiji wurin hutawa, da wurin zaman zatin Allah. Na riga na yi shiri domin ginin, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 Sarki Dawuda ya miƙe tsaye ya ce, “Ku saurare ni, ’yan’uwana da kuma mutanena. Na yi niyya in gina gida a matsayin wurin hutu domin akwatin alkawarin Ubangiji, domin zatin Allahnmu, na kuma yi shiri don in gina shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Da wahala mai yawa na yi tanadi domin Haikalin Ubangiji, zinariya wajen talanti dubu ɗari (100,000), da azurfa kuma wajen talanti zambar dubu (1,000,000), domin gina Haikalin Ubangiji. Bayan wannan akwai tagulla da ƙarfe masu tarin yawa. Na kuma tanada katakai da duwatsu. Kai kuma sai ka ƙara a kansu.