Haka kuwa Sulemanu ya yi dukan kayayyakin nan da suke cikin Haikalin Allah, duk da zinariya tsantsa aka yi su. bagade na zinariya tebur don ajiye gurasar ajiyewa alkukai tare da fitilunsu na zinariya tsantsa, domin a kunna su a gaban Wuri Mafi Tsarki na ciki kamar yadda aka tsara furanni fitilu arautaki hantsuka daruna cokula farantan wuta ƙofofi na can ciki ƙofofi na waje.