1 Tarihi 27:1 - Littafi Mai Tsarki1 Ga lissafin kawunan iyalin Isra'ilawa, da shugabannin dangi, da jama'a masu gudanar da ayyukan mulki. A kowane wata akan sauya aikin ƙungiyar mutum dubu ashirin da dubu huɗu (24,000), a ƙarƙashin shugaban aiki na wannan wata. Kowane wata akan sauya, wata ƙungiya ta kama aiki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 Wannan shi ne jerin Isra’ilawa, kawunan iyalai, shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da manyan ma’aikatansu, waɗanda suka yi wa sarki hidima a dukan abin da ya shafi ɓangarorin mayaƙan da suke aiki wata-wata a dukan shekara. Kowane sashe yana da mutane 24,000. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗannan su ne shugabanni don kowane wata. Wata na 1, Yashobeyam, ɗan Zabdiyel. (Shi daga dangin Feresa na kabilar Yahuza ne.) Wata na 2, Dodai, ɗan Ahowa. (Miklot yake bi masa a shugabancin.) Wata na 3, Benaiya, ɗan Yehoyada firist. Shugaba ne daga cikin sanannun nan “talatin.” (Ɗansa Ammizzabad ya gāje shi a shugabancin ƙungiya.) Wata na 4, Asahel, ƙanen Yowab. (Ɗansa Zabadiya ya gāje shi.) Wata na 5, Shimeya, daga zuriyar Izhara. Wata na 6, Aira, ɗan Ikkesha, daga Tekowa. Wata na 7, Helez, mutumin Ifraimu, daga Felet. Wata na 8, Sibbekai, daga garin Husha. (Shi daga dangin Zera ne, na kabilar Yahuza.) Wata na 9, Abiyezer, daga Anatot na kabilar Biliyaminu. Wata na 10, Maharai, daga Netofa. (Shi ma daga dangin Zera ya fito.) Wata na 11, Benaiya, daga Firaton na kabilar Ifraimu. Wata na 12, Heled, daga Netofa. (Shi daga zuriyar Otniyel ne.)