1 Tarihi 26:26 - Littafi Mai Tsarki26 Shi wannan Shelomit da 'yan'uwansa suke lura da kyautai waɗanda sarki Dawuda, da shugabannin, gidajen kakanni, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da shugabannin sojoji suka keɓe ga Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202026 Shelomit da danginsa su ne suke lura da dukan baitulmali don kayayyakin da Sarki Dawuda ya keɓe, ta wajen kawunan iyalai waɗanda suke shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da kuma wajen sauran shugabannin mayaƙa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Da wahala mai yawa na yi tanadi domin Haikalin Ubangiji, zinariya wajen talanti dubu ɗari (100,000), da azurfa kuma wajen talanti zambar dubu (1,000,000), domin gina Haikalin Ubangiji. Bayan wannan akwai tagulla da ƙarfe masu tarin yawa. Na kuma tanada katakai da duwatsu. Kai kuma sai ka ƙara a kansu.