1 Tarihi 25:1 - Littafi Mai Tsarki1 Dawuda fa da shugabannin Lawiyawa suka zaɓi waɗansu daga cikin 'ya'yan Asaf, maza, da na Heman, da na Yedutun domin su raira waƙa da garayu, da molaye, da kuge. Ga waɗanda suka yi wannan hidima. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 Dawuda tare da shugabannin mayaƙa, suka keɓe waɗansu daga ’ya’yan Asaf, Heman da Yedutun don hidimar yin annabci, suna amfani da garayu, molaye da ganguna. Ga jerin mutanen da suka yi wannan hidima. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bisa ga ka'idar da tsohonsa Dawuda ya tsara, sai Sulemanu ya karkasa firistoci ƙungiya ƙungiya domin su yi hidima, Lawiyawa kuma bisa ga matsayinsu na yin yabo da hidima a gaban firistoci, kamar yadda aka wajabta kowace rana. Matsaran ƙofa kuma aka karkasa su ƙungiya ƙungiya bisa ga yawan ƙofofin, gama haka Dawuda, mutumin Allah, ya umarta.
Waɗannan su ne shugabannin ƙungiyoyi ashirin da huɗu, na goma sha biyu biyu, bisa ga yadda aka tsara su ga aikin: 1. Yusufu daga iyalin Asaf 2. Gedaliya 3. Zakku 4. Zeri 5. Netaniya 6. Bukkiya 7. Asharela 8. Yeshaya 9. Mattaniya 10. Shimai 11. Uzziyel 12. Hashabiya 13. Shebuwel 14. Mattitiya 15. Yeremot 16. Hananiya 17. Yoshbekasha 18. Hanani 19. Malloti 20. Eliyata 21. Hotir 22. Giddalti 23. Mahaziyot 24. Romamtiyezer