1 Tarihi 24:6 - Littafi Mai Tsarki6 Shemaiya, ɗan Netanel marubuci, Balawe, ya rubuta su a gaban sarki da shugabanni, da Zadok firist, da Ahimelek ɗan Abiyata, da shugabannin gidajen kakannin firistoci, da Lawiyawa. Aka ɗauki gida guda daga gidajen kakannin Ele'azara, aka kuma ɗauki ɗaya daga gidajen kakannin Itamar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga yadda aka shirya ƙungiyoyin iyali ashirin da huɗu su sami aikinsu: 1. Yehoyarib 2. Yedaiya 3. Harim 4. Seyorim 5. Malkiya 6. Mijamin 7. Hakkoz 8. Abaija 9. Yeshuwa 10. Shekaniya 11. Eliyashib 12. Yakim 13 Huffa 14. Yeshebeyab 15. Bilga 16. Immer 17. Hezir 18. Haffizzez 19. Fetahiya 20. Yehezkel 21. Yakin 22. Gamul 23. Delaiya 24. Ma'aziya.