1 Tarihi 24:4 - Littafi Mai Tsarki4 Tun da yake akwai manyan mutane da yawa a zuriyar Ele'azara fiye da zuriyar Itamar, sai suka karkasa su haka, shugabannin gidajen kakannin zuriyar Ele'azara mutum goma sha shida, na zuriyar Itamar kuwa su takwas, bisa ga gidajen kakanninsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 Akwai ɗumbun shugabanni a cikin zuriyar Eleyazar fiye da zuriyar Itamar, aka kuma karkasa su haka, kawuna goma sha shida daga zuriyar Eleyazar da kuma kawuna iyalai takwas daga zuriyar Itamar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A zamanin Yoyakim babban firist, waɗannan su ne shugabannin iyalin firistoci, na wajen Seraiya, Meraiya ne na wajen Irmiya, Hananiya ne na wajen Ezra, Meshullam ne na wajen Amariya, Yehohanan ne na wajen Malluki, Jonatan ne na wajen Shebaniya, Yusufu ne na wajen Harim, Adana ne na wajen Merayot, Helkai ne na wajen Iddo, Zakariya ne na wajen Ginneton, Meshullam ne na wajen Abaija, Zikri ne na wajen Miniyamin da Mowadiya, Filtai ne na wajen Bilga, Shimeya ne na wajen Shemaiya, Yehonatan ne na wajen Yoyarib, Mattenai ne na wajen Yedaiya, Uzzi ne na wajen Sallai, Kallai ne na wajen Amok, Eber ne na wajen Hilkiya, Hashabiya ne na wajen Yedaiya, Netanel ne.