1 Tarihi 24:3 - Littafi Mai Tsarki3 Sai Dawuda da Zadok daga zuriyar Ele'azara, da Ahimelek daga zuriyar Itamar suka karkasa su bisa ga ƙayyadaddun lokatansu na yin aiki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Tare da taimakon Zadok zuriyar Eleyazar da Ahimelek wani zuriyar Itamar. Dawuda ya karkasa su zuwa ɓangarori don aikinsu bisa ga hidima. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bisa ga ka'idar da tsohonsa Dawuda ya tsara, sai Sulemanu ya karkasa firistoci ƙungiya ƙungiya domin su yi hidima, Lawiyawa kuma bisa ga matsayinsu na yin yabo da hidima a gaban firistoci, kamar yadda aka wajabta kowace rana. Matsaran ƙofa kuma aka karkasa su ƙungiya ƙungiya bisa ga yawan ƙofofin, gama haka Dawuda, mutumin Allah, ya umarta.