Ga dai ƙungiyoyin firistoci da na Lawiyawa, suna nan domin yin hidima a Haikalin Allah, ga kuma gwanaye na kowace irin sana'a suna tare da kai don yin kowane irin aiki. Shugabanni da dukan jama'a suna ƙarƙashinka duka.”
Sai Lawiyawa da dukan Yahuza suka yi yadda Yehoyada, firist, ya umarta. Kowannensu ya kawo mutanensa waɗanda ba su aiki ran Asabar, da masu kama aiki ran Asabar, gama Yehoyada, firist, bai sallami ƙungiyoyin ba.
Hezekiya kuma ya raba firistoci da Lawiyawa kashi kashi, ko wanne da hidimarsa, firistoci da Lawiyawa, don hadayu na ƙonawa da na salama, su yi hidima a ƙofofin Ubangiji, don su yi godiya da yabo.