22 Na wajen Izhara, shi ne Shelomit, na wajen Shelomit, shi ne Yahat.
22 Daga mutanen Izhar, Shelomot; daga ’ya’yan Shelomot maza, Yahat.
Ɗan Izhara shi ne Shelomit, shugaba.
Shi wannan Shelomit da 'yan'uwansa suke lura da kyautai waɗanda sarki Dawuda, da shugabannin, gidajen kakanni, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da shugabannin sojoji suka keɓe ga Allah.
Iyalan Kohat su ne iyalin Amramawa, da na Izharawa, da na Hebronawa, da na Uzziyelawa. Waɗannan su ne iyalan Kohatawa.
Ga 'ya'yan Kohat, maza, bisa ga iyalansu, da Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel.
'Ya'yan Izhara, su ne Kora, da Nefeg, da Zikri.
Na wajen Rehabiya, shi ne Isshiya,
Na wajen Hebron, su ne Yeriya na fari, da Amariya, da Yahaziyel, da Yekameyam.
'Ya'yan Amram kuwa, su ne Haruna, da Musa, da Maryamu. 'Ya'yan Haruna, maza, su ne Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar.