1 Tarihi 23:5 - Littafi Mai Tsarki5 dubu huɗu (4,000) su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu (4,000) kuma za su zama masu raira yabbai ga Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda ya yi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20205 Dubu huɗu su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu kuma su yabi Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda na tanada saboda wannan manufa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bisa ga ka'idar da tsohonsa Dawuda ya tsara, sai Sulemanu ya karkasa firistoci ƙungiya ƙungiya domin su yi hidima, Lawiyawa kuma bisa ga matsayinsu na yin yabo da hidima a gaban firistoci, kamar yadda aka wajabta kowace rana. Matsaran ƙofa kuma aka karkasa su ƙungiya ƙungiya bisa ga yawan ƙofofin, gama haka Dawuda, mutumin Allah, ya umarta.