18 Ɗan Izhara shi ne Shelomit, shugaba.
18 ’Ya’yan Izhar maza su ne, Shelomit ne ɗan fari.
Shi wannan Shelomit da 'yan'uwansa suke lura da kyautai waɗanda sarki Dawuda, da shugabannin, gidajen kakanni, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da shugabannin sojoji suka keɓe ga Allah.
Na wajen Izhara, shi ne Shelomit, na wajen Shelomit, shi ne Yahat.
'Ya'ya maza na Kohat kuwa, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel. Kohat ya rayu shekara ɗari da talatin da uku.
Ɗan Eliyezer shi ne Rehabiya, shugaba, shi Eliyezer ba shi da waɗansu 'ya'ya, amma Rehabiya yana da 'ya'ya da yawa.
'Ya'yan Hebron, maza, su ne Yeriya, shi ne babba, da Amariya na biyu, da Yahaziyel na uku, da kuma Yekameyam na huɗu.