Mutanen Yahuza suka je wurin Joshuwa a Gilgal, sa'an nan Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, ya ce masa, “Ka dai san maganar da Ubangiji ya yi wa Musa, mutumin Allah, a Kadesh-barneya a kaina.
Sai Yeshuwa ɗan Yehozadak tare da 'yan'uwansa, firistoci, da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel tare da 'yan'uwansu, suka tashi suka gina bagaden Allah na Isra'ila domin a miƙa hadayu na ƙonawa kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, mutumin Allah.