1 Tarihi 22:7 - Littafi Mai Tsarki7 Dawuda kuwa ya ce wa Sulemanu, “Ɗana, na ƙudura a zuciyata in gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Dawuda ya ce wa Solomon, “Ɗana, na yi niyya a zuciyata in gina gida saboda Sunan Ubangiji Allahna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga shi dai, na yi niyyar gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe masa shi, domin a riƙa ƙona masa turare mai daɗin ƙanshi, inda kuma za a riƙa ajiye gurasar ajiyewa dukan lokaci, don kuma a riƙa miƙa hadayun ƙonawa safe da yamma, da ranakun Asabar, da na amarya wata, da kuma a lokatan ƙayyadaddun idodin Ubangiji Allahnmu, yadda dai aka faralta a riƙa yi a cikin Isra'ila.