Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 22:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Sai Dawuda ya kira Sulemanu ɗansa, ya yi masa wasiyyar gina Haikalin Ubangiji, Allah na Isra'ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Sa’an nan ya kira ɗansa Solomon ya umarce shi yă gina gida domin Ubangiji, Allah na Isra’ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 22:6
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Na gama ka da Allah, da kuma Almasihu Yesu, wanɗa zai yi wa rayayyu da matattu shari'a, na kuma gargaɗe ka saboda bayyanarsa da kuma mulkinsa,


Na gama ka da Allah, da Almasihu Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala'iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka yi kome da tāra.


har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi aka kai shi Sama, bayan ya yi umarni ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa.


Sai Ubangiji ya umarci Joshuwa ɗan Nun ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai jama'ar Isra'ila a ƙasar da na rantse zan ba su, ni kuma da kaina zan tafi tare da kai.”


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Lokacin rasuwarka ya yi, sai ka kira Joshuwa, ku shigo alfarwa ta sujada, don in ba shi ragamar mulki.” Sai Musa da Joshuwa suka tafi, suka shiga alfarwa ta sujada.


Ya ɗibiya hannuwansa a kansa, ya keɓe shi kamar yadda Ubangiji ya umarta.


Fir'auna kuma ya umarci mutanensa a kan Abram, su raka shi da matarsa, da dukan abin da yake da shi.


Sa'ad da lokacin rasuwar Dawuda ya gabato, sai ya yi wa ɗansa Sulemanu gargaɗi na ƙarshe, ya ce,


Sa'ad da sarki yake zaune a gidansa, Ubangiji kuma ya hutasshe shi daga fitinar abokan gābansa da suke kewaye da shi,


Sa'ad da Dawuda yake zaune a fādarsa, sai ya ce, wa annabi Natan, “Ga shi, ni ina zaune a cikin gidan da aka yi da itacen al'ul, amma akwatin alkawarin Ubangiji yana cikin alfarwa.”


Sarki Dawuda fa ya miƙe tsaye, ya ce, “Ku saurare ni, ku 'yan'uwana, da jama'ata. Na yi niyya a zuciyata in gina wa akwatin alkawari na Ubangiji wurin hutawa, da wurin zaman zatin Allah. Na riga na yi shiri domin ginin,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ