1 Tarihi 22:14 - Littafi Mai Tsarki14 Da wahala mai yawa na yi tanadi domin Haikalin Ubangiji, zinariya wajen talanti dubu ɗari (100,000), da azurfa kuma wajen talanti zambar dubu (1,000,000), domin gina Haikalin Ubangiji. Bayan wannan akwai tagulla da ƙarfe masu tarin yawa. Na kuma tanada katakai da duwatsu. Kai kuma sai ka ƙara a kansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 “Na sha wahala da yawa don in yi tanadi talentin dubu ɗari na zinariya, talenti miliyon na azurfa, ɗumbun tagulla da ƙarfe da suka wuce ƙirge da katako da dutse saboda haikalin Ubangiji. Za ka iya ƙara su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A halin yanzu dai na riga na yi iyakacin ƙoƙarina, har na tanada waɗannan abubuwa saboda Haikalin Allahna, wato zinariya saboda kayayyakin zinariya, azurfa saboda kayayyakin azurfa, tagulla saboda kayayyakin tagulla, baƙin ƙarfe saboda kayayyakin baƙin ƙarfe, itace kuwa saboda kayayyakin itace, da duwatsu da yawa masu daraja, da masu launi iri iri.