(A dā a Isra'ila, idan wani yana so ya yi tambaya ga Allah, sai ya ce, “Zo, mu tafi wurin maigani.” Gama wanda ake ce da shi annabi yanzu, a dā akan ce da shi maigani.)
Sai ya zaunar da Lawiyawa a Haikalin Ubangiji, masu kuge, da molaye, da garayu, bisa ga umarnin Dawuda, da na Gad, maigani na sarki, da na annabi Natan. Gama umarnin daga wurin Ubangiji ya zo ta wurin annabawansa.