Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 21:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Dawuda fa ya ce wa Yowab da sauran shugabannin jama'a, “Ku tafi, ku ƙidaya jama'ar Isra'ila tun daga Biyer-sheba har zuwa Dan, ku kawo mini labari don in san yawansu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Saboda haka Dawuda ya ce wa Yowab da shugabannin mayaƙa, “Ku tafi ku ƙidaya Isra’ilawa daga Beyersheba zuwa Dan. Ku kawo mini labarin saboda in san su nawa ne.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 21:2
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Don kada kaina yă kumbura kuma saboda mafifitan wahayan da aka yi mini, sai aka saka mini wata cuta, wadda ta zama mini ƙaya, jakadan Shaiɗan, don yă riƙa wahalshe ni, don kada kaina ya kumbura.


Girmankan mutum zai jawo masa ƙasƙanci, amma za a girmama mai tawali'u.


Sai suka ba da umarni a yi shela a Isra'ila duka, tun daga Biyer-sheba, har zuwa Dan, cewa sai mutane su zo Idin Ƙetarewa na Ubangiji Allah na Isra'ila a Urushalima, gama jama'a mai yawan gaske ba su zo wurin yin idin kamar yadda aka umarta ba.


Mutanen Yahuza da na Isra'ila suka zauna lafiya tun daga Dan har Biyersheba. Kowa ya yi zamansa a gida dukan kwanakin Sulemanu.


Ubangiji kuwa ya aika da annoba a kan Isra'ila tun da safe har zuwa lokacin da aka ƙayyade. Mutum dubu saba'in (70,000) suka mutu daga Dan zuwa Biyer-sheba.


Shawarata ita ce a tattara maka dukan Isra'ilawa tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba, yawansu kamar yashi a bakin teku. Kai kuma da kanka ka tafi wurin yaƙin.


wato in mayar wa Dawuda da sarautar gidan Saul. In kafa kursiyin Dawuda a kan Isra'ila da kan Yahuza tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba.”


Dukan mutanen Isra'ila fa daga wannan kusurwar ƙasa zuwa wancan, sun tabbata Sama'ila annabin Ubangiji ne.


Dukan jama'ar Isra'ila fa suka fito tun daga Dan a arewa har zuwa Biyer-sheba a kudu da kuma Gileyad daga gabas. Suka hallara gaba ɗaya a gaban Ubangiji a Mizfa.


Ibrahim ya tashi da sassafe, ya kuma ɗauki gurasa da salkar ruwa, ya bai wa Hajaratu, ya ɗora kafaɗarta. Sai ya ba ta ɗanta, ya sallame ta. Ta tafi ta yi ta yawo cikin jejin Biyer-sheba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ