Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 21:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Dawuda ya ɗaga idonsa, sai ya ga mala'ikan Ubangiji yana tsakanin sama da ƙasa, da takobinsa a zare a hannunsa a kan Urushalima. Sa'an nan Dawuda tare da dattawa suka fāɗi rubda ciki, suna saye da tufafin makoki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Sai Dawuda ya ɗaga ido ya ga mala’ikan Ubangiji tsaye tsakanin sama da duniya, da takobi a zāre a hannunsa ya miƙa a kan Urushalima. Sai Dawuda da dattawa, saye da rigunan makoki suka fāɗi rubda jiki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 21:16
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki a gaban dukan taron jama'ar Isra'ilawa.


Da Ahab ya ji wannan magana, sai ya yage tufafinsa, ya sa na makoki, ya yi azumi, ya kwanta a tsummokin makoki, ya tashi yana tafiya a hankali.


Da sarki Hezekiya ya ji wannan magana, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa rigar makoki, sa'an nan ya shiga Haikalin Ubangiji.


Sa'an nan Elisha ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubangiji, ka buɗe idanunsa ya gani.” Ubangiji kuwa ya buɗe idanun saurayin, sai ga dutsen cike da dawakai da karusan wuta kewaye da Elisha.


Ubangiji kuwa ya buɗe idanun Bal'amu, ya ga mala'ikan Ubangiji yana tsaye a hanya da takobi zāre a hannunsa. Sai ya sunkuyar da kansa, ya fāɗi rubda ciki.


Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki, suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin 'yan adam duka, za ka yi fushi da dukan taron jama'a saboda zunubin mutum ɗaya?”


Ya kori mutum kuma a gabashin gonar Aidan, ya kafa kerubobi, da kuma takobi mai harshen wuta wanda yake jujjuyawa ko'ina don su tsare hanya zuwa itacen rai.


Sa'ad da harshen wutar ya hau zuwa samaniya daga bagaden, sai mala'ikan Ubangiji ya hau zuwa sama ta cikin harshen wutar bagaden. Manowa da matarsa sun gani, suka fāɗi a fuskokinsu a ƙasa.


Sa'ad da suke karkashewar, aka bar ni, ni kaɗai, sai na faɗi rubda ciki, na yi kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah za ka hallaka dukan sauran Isra'ilawa saboda zafin fushinka a kan Urushalima?”


Zan ƙarfafa hannuwan Sarkin Babila, amma hannuwan Fir'auna za su shanye. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na sa takobina a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai miƙe shi a kan ƙasar Masar.


Da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji yana tsaye kan hanya da takobi zare a hannunsa, sai ta kauce daga hanya, ta shiga saura. Bal'amu kuwa ya buge ta don ya komar da ita a hanyar.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ