1 Tarihi 21:13 - Littafi Mai Tsarki13 Dawuda kuwa ya ce wa Gad, “Na shiga uku, gara in fāɗa a hannun Ubangiji, gama shi mai yawan jinƙai ne, kada ka bar ni in faɗa a hannun mutum.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 Dawuda ya ce wa Gad, “Na shiga uku. Bari in fāɗa a hannuwan Ubangiji, gama jinƙansa yana da girma sosai; amma kada ka bari in fāɗa a hannuwan mutane.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Dukan barorin sarki da mutanen lardunan sarki sun sani duk wanda ya tafi wurin sarki a shirayi na ciki, ba tare da an kira shi ba, to, doka ɗaya ce take kan mutum, wato kisa, ko mace ko namiji, sai dai wanda sarki ya miƙa wa sandan sarauta na zinariya don ya rayu. Kwana talatin ke nan ba a kira ni in tafi wurin sarki ba.”
Saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ina roƙonka, ya Ubangiji, ashe, dā ma can ban faɗa ba, kafin in bar gida, cewa irin abin da za ka yi ke nan? Ai, dalilin da ya sa na yi iyakar ƙoƙarina in gudu zuwa Tarshish ke nan. Na sani kai mai taushin hali ne, mai jinƙai, mai haƙuri. Kai kullum mai alheri ne, a shirye kake kuma ka dakatar da nufinka na yin hukunci.