Sai na ji wata murya mai ƙara a Sama tana cewa, “A yanzu fa, ceto, da ƙarfi, da mulki na Allahnmu, da kuma ikon Almasihunsa sun bayyana, don an jefa mai ƙarar 'yan'uwanmu a ƙasa, shi da yake ƙararsu dare da rana a gun Allahnmu.
Yowab ɗan Zeruya ne ya fara ƙidayar, amma bai gama ba. Allah ya hukunta wa Isra'ila saboda wannan ƙidaya, saboda haka ba za a taɓa samun cikakken adadi a lissafin da suke a ajiye na fādawan sarki Dawuda ba.
Waɗannan duka su ne zuriyar Ashiru, su ne kuma shugabannin gidajen kakanninsu. Zaɓaɓɓun jarumawa ne su, manyan sarakuni. Yawansu da aka lasafta bisa ga asalinsu don yaƙi su dubu ashirin da dubu shida ne (26,000).