Feniyel shi ne mahaifin Gedor, Ezer kuwa shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne 'ya'yan Hur, maza, wato ɗan farin Efrata, zuriyarsa ne suka kafa Baitalami.
“ ‘Ke ma Baitalami, ta kasar Yahuza, Ko kusa ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin manyan garuruwan Yahuza ba, Domin daga cikinki za a haifi wani mai mulki, Wanda zai zama makiyayin jama'ata, Isra'ila.’ ”
Sa'ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,
Dukan jama'a suka ce, “Mu ne shaidu, Ubangiji yă sa matar da za ta zo gidanka ta zama kamar Rahila da Lai'atu waɗanda suka gina gidan Isra'ila. Allah ya arzuta ka cikin Efrata, yă sa ka yi suna a cikin Baitalami,
A zamanin da mahukunta suke mulkin Isra'ila, aka yi yunwa a ƙasar. Sai wani mutumin Baitalami a Yahudiya ya yi ƙaura zuwa ƙasar Mowab, shi da matarsa, da 'ya'yansa maza biyu.